<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>484</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1)Mun gode Allah Ubangiji,
 Domin ƙamnarka,
 Yadda kai ka bada Ɗanka Yesu
 Domin cetonmu.

[V2]
 KORUS
 I, muna yin roƙo
 Ya Ubangijinmu,
 Ka ji addu'armu,
 Cika mu da ƙamnarka.

[V3]
 2) Muna roƙo Ubangiji Yesu
 Ҡara ƙamnarmu,
 Mu dai ba mu cika ƙamnar juna
 Yadda ka ke so.
 Korus

[V4]
 3) Muna roƙo Ruhun Ubangiji
 Cika zuciyarmu,
 Cika mu da nufin yin biyayya
 Da maganarka.
 Korus

[V5]
 4) Allah Uba, Yesu Mai Cetonmu
 Ruhu Mai Tsarki,
 Duka uku sai ku taimake mu
 Muna yin addu'a.
 Korus</lyrics>
<title>Mun Gode Allah Ubangiji, Domin Ƙamnarka LW484</title>
</song>